30 Oktoba 2025 - 10:35
Source: ABNA24
Iran Ta Fitar Da Man Fetur Na Farko Zuwa Afghanistan Ta Jirgin Kasa

Iran ta fitar da man fetur na farko zuwa Afghanistan ta jirgin kasa, a wani mataki da ake ganin yana da matukar muhimmanci ga fadada cinikayya da hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jakadan Iran a Kabul, Ali Reza Bikdeli, ya sanar da cewa wannan shiri ya nuna sabon farawa na karfafa musayar tattalin arziki da sufuri tsakanin Iran da Afghanistan, yana mai jaddada muhimmancin aikin wajen sauƙaƙa jigilar kayayyaki da muhimman kayayyaki tsakanin bangarorin biyu.

Your Comment

You are replying to: .
captcha